An ɗaura auren Jaruma Zuwaira Musa - Kalli hotuna
Jaruma a Kannywood, Zuwaira Musa, ta bi sahun masu yin aure a ƙarshen wannan shekara ta 2024 domin kuwa a jiya Asabar 7 ga Disamba ne aka ɗaura auren Jarumar tare da angonta Buhari Umar (General).
An ɗaura auren ne a masallacin Juma’a dake Unguwar Na’ibawa a cikin garin Kano da misalin ƙarfe ɗaya na rana.
Tun kafin ranar ɗaura auren jarumar ta shirya wani gagarumin taro na murnar shagalin bikin nata.
A ranar Juma’a aka yi taron bikin a titin Lawan Dambazau inda jarumai mata da yawa suka halarci taron bikin.
Cikin waɗanda suka halarci taron bikin akwai Hadiza Kabaraz Asma’u Sani, Maijidda Abbas da sauran su.
Muna fatan Allah ya bada zaman lafiya da kwanciyar hankali a zaman auren.