An Buɗe Shafin Ɗaukar Ma’aikata a Ƙungiyar Agaji ta Save the Children
Save the Children na ɗaya daga cikin manyan ƙungiyoyi masu zaman kansu a Najeriya da suka himmatu wajen taimakon yara masu bukata. Ƙungiyar tana gudanar da shirye-shirye a ƙasashe sama da 120, tana ceto yara ƙanana daga yunwa, wahala, da kuma fafutukar kare haƙƙinsu, tare da taimaka musu su cimma burinsu.
A Najeriya, Save the Children tana aiki ne saboda ɗaya daga cikin yara biyar a ƙasar na mutuwa kafin su kai shekaru biyar. Har ila yau, kusan kashi 40 cikin 100 na yara ba sa zuwa makaranta, kuma ana tilasta musu yin aiki don rayuwa. Bugu da ƙari, kusan yara miliyan biyu sun rasa iyaye ɗaya ko duka biyun saboda kamuwa da cutar kanjamau (AIDS).
A halin yanzu, ƙungiyar Save the Children ta buɗe shafin ɗaukar sabbin ma'aikata a fannoni daban-daban kamar yadda za ku gani a ƙasa.
1. Child Protection Information Management System (CPIMS) Assistant - PLANE, Kano
2. Child Protection Officer, ECW-FER
3. Child Protection Coordinator - ROOSC
4. Education Programme Manager, Borno
5. Driver - Kano
6. Consultant - Organisation Development (Nigeria National Only)
7. Driver - Jigawa
8. Supply Chain Manager
9. Finance Intern
10. Child Protection Officer - ROOSC