Hukumar NITDA Tare Da Haɗin Gwiwar JICA Sun Bude Shafin Cike Shirin iHatch Hub Managers Upskilling Programme na Matasan Najeriya
Ana sanar da duk masu sha’awar samun gurbin horon iHatch Hub Managers Upskilling Programme su garzaya domin neman gurbi. Wannan shiri na musamman wanda hukumar National Information Technology Development Agency (NITDA) tare da haɗin gwiwar Japan International Cooperation Agency (JICA) suka ƙaddamar, yana nufin samar wa shugabannin cibiyoyin ƙirƙira dabaru, ilimi, da hanyoyin haɗin gwiwa don bunƙasa ci gaban fasaha a yankunansu.
Manufar shirin ita ce ba da horo na musamman a fannin gudanar da cibiyoyi da tallafa wa 'yan kasuwa, samar da hanyoyi don gina al'umma ta fasaha, da kuma samar da haɗin kai a matakin ƙasa da ƙasa.
Za a rufe neman gurbin shiga wannan shiri ranar 15 ga Disamba, 2024. Don neman ƙarin bayani ko cika fam ɗin neman gurbi, za ku iya ziyartar shafin yanar gizon su ko aiko saƙo zuwa info@startup.gov.ng. Kada ku yi jinkiri, ku shiga wannan dama don zama cikin waɗanda za su ciyar da Najeriya gaba ta fuskar kirkira da fasaha.
Yadda Zaku Cike
Domin Cikewa ku latsa shafin yanar gizo gizo dake a kasa
https://programs.startup.gov.ng/ihatch?fbclid
Allah Yasa Mu Dace Baki Daya