Jama’a sun nuna mini kara a bikin auren ƙanwata, inji Raihan Qamshi
Tun bayan bayyanar hotunan bikin Sa’adatu, ƙanwar Jaruma Raihan Imam Ahmad Qamshi jama’a suke ta kiran ta tare da yi mata fatan alheri tare da tambayar ko ta yi aure ne.
Wasu kuma na yi mata fatan alheri ne a zaton su auren ta ne, har ma aka riƙa yaɗawa a kafafen sada zumunta ana ta cewa Jaruma Raihan Imam Ahmad Qamshi ta yi aure don haka ne ake ta yi mata fatan alheri tare da addu’ar Allah ya zaunar da ita a gidan mijinta lafiya.
Mujallar fim ta halarci taron bikin auren da aka gudanar kuma aka yi shagulgulan bikin na ƙasaita.
Kusan duk wata jaruma da take ji da kanta a cikin masana’antar finafinan ta Kannywood ta halarci taron bikin, don kuwa za a iya cewa an daɗe ba a yi irin wannan taron bikin ba a Kannywood.
Bayan bikin dai mun samu tattaunawa da Raihan, don bayyana wa duniya matsayin ta a game da auren, inda muka fara da tambayar ta kan maganar da take yawo na cewar ta yi aure.
To da farko dai zan fara da cewa Alhamdulillahi, ina ƙara godiya ga Allah da ya ba ni ikon gudanar da wannan taro, wanda kuma taro ne da ban yi tsammanin zai tafi haka ba, sai kuma abin ya zo ya bani mamaki, saboda ya tafi yadda ban taɓa tsammani ba.
“Taro ne na shirya shi na bikin ƙanwata wacce nake jin ta tamkar ‘yar da na haifa, don haka taron ba na bikina ba ne kamar yadda mutane suke faɗa, don tun da hotunan bikin suka yaɗu mutane suna ta kirana suna yi mini fatan alheri su a zaton su auren nawa ne. Wasu suna kira na su tambaye ni, wasu kuma kawai suna yi mini fatan alheri ne sun zata nawa ne.
“Amma dai gaskiya ita wannan amarya Sa’adatu ƙanwa ta ce , ita ce ƙarama a ɗakin mu, kuma gaskiya dai ba ni da kamar ta, ina son ta sosai, don na tashi da ita tun tana ƙarama, kusan zan iya cewa na raine ta kusan dai ina alfahari da yarinyar nan Sa’adatu sosai, saboda jinin jiki na ce, kuma ta kasance yarinya mai biyayya daidai gwargwado yadda ko ni na haife ta iya biyayyar da za ta yi mini kenan.
“Sannan kuma duk wani wanda ya san ta ko yake zuwa gidan mu, to za ka yi alfahari da Sa’adatu, saboda yarinya ce mai biyayya, wannan ya sa na ga duk abin da na yi mata a cikin sabgar bikin nan ban yi asara a cikin rayuwa ta ba, don duk wani abu da zan yi wa dan da zan haifa to shi zan yi mata.”