Jarumar Kannywood, Fa’iza Abdullahi, wadda aka fi sani da Bilki a cikin shirin ‘Daɗin Kowa’ na gidan talbijin na Arewa 24, ta bayyana irin jin daɗin da take yi a duk lokacin da ta fito a matsayin masifaffiya a cikin fim.
Jarumar, wadda ke fitowa a matsayin matar Kofur Audu a shirin, ta bayyana haka ne ga mujallar Fim a lokacin tattaunawar ta da wakilin mu.
FIM: Mu fara da jin tarihin rayuwar ki.
FA’IZA: Na farko, suna na Fa’iza Abdullahi. An haife ni ne a cikin Jihar Bauchi, a wani gari da ake kira Jalaf a Ƙaramar Hukumar Damban. A can na yi karatu na girma duk a can.
A yanzu dai ban wuce shekara 26 ba, sai kuma a yanzu da na kasance a garin Kano ina gudanar da sana’a ta ta aikin fim.
FIM: Shin fim ne ya kawo ki Kano kuma a wane lokacin kika zo?
FA’IZA: To gaskiya, zuwa na Kano zai kai shekara bakwai a yanzu kuma harkar fim ce ta kawo ni Kano, don in ban da ta dalilin fim ban san kowa a Kano ba, ban ma taɓa zuwa ba sai ta sanadin zan yi fim.
FIM: Da yake an fi sanin Fa’iza Abdullahi a cikin shirin ‘Daɗin Kowa’ a matsayin matar Kofur Audu, ko kin taɓa yin wani fim ɗin kafin ki fara ‘Daɗin Kowa’?
FA’IZA: Gaskiya ban taɓa yin wani fim ba sai ‘Daɗin Kowa’, don da shi na fara. Ba zan manta ba lokacin da na zo garin Kano haka, ina zuwa Zoo Road akwai wani da na sani wanda shi ne darakta a fim ɗin a lokacin, nakan je na gaishe su, duk da ban ma san shi waye ba a lokacin, sai wata rana ya kira ni ya ce na zo ana nema na zan yi sin ɗaya a wani aiki, to ban ma san yadda abin yake ba sai da na je. To da haka na fara, har aka zo daga baya ake kira na lokaci zuwa lokaci.