Nigeria Customs Service ta Buɗe Shafin Daukar Sabbin Ma'ikata 2024/2025
Meman Aiki Daga wannan hukumar ta Custom a Nigerian.
Kamar yadda muka Saba kawo maku labari Akan sababbin damar daukar aiki yauma GA wata damar !!!
Hukumar Fasa Kwari ta Najeriya (Nigeria Customs Service) tana sanar da matasa masu sha’awar shiga aikin hukumar cewa an bude manhajar daukar ma’aikata yau, Juma’a 27 ga Disamba, 2024. Za a rufe neman aikin ranar Talata, 2 ga Janairu, 2025. Wannan dama ce ga matasa ‘yan Najeriya masu sha’awar shiga aikin kwastam don taimaka wa ci gaban kasa.
Masu sha’awar neman wannan aiki su kasance suna da shaida ta kammala karatu da kuma cancanta bisa ga bukatun hukumar.
Ga Yadda Za Ku Cike Neman wannan Aikin cikin sauki
Da farko dai !!
1. Shiga shafin yanar gizo na hukumar a: http://www.vacancy.customs.gov.ng
2. Cike dukkan bayanai da ake bukata da gaskiya.
3. Tabbatar kun gabatar da dukkan takardun da ake nema kafin wa’adin rufewa.
Kuyi share zuwa ga Yan uwa domin su amfana !!