Producer Musty Fashion ya yi rashin mahaifi Allah yajikanshi da rahama
A ranar Alhamis data gabata, Allah ya ɗauki ran Alhaji Hussaini Khalid Kano, mahaifin furodusa kuma jarumi a Kannywood, Mustapha Hussaini, wanda aka fi sani da Musty Fashion.
Alhaji Hussaini ya rasu da misalin ƙarfe 6:46 na safe a asibitin Malam Adam Algarƙawi mai suna Attatbiq da ke unguwar Kinkinau, Kaduna, bayan ‘yar gajeruwar jinya da ya yi.
Shekarun sa kimanin 77 a duniya, kuma ya bar ‘ya’ya 23.
An yi masa jana’iza da misalin ƙarfe 1:00 na rana a masallacin Malam Algarƙawi da ke Kinkinau.
‘Yan fim da suka je ta’aziyya sun haɗa da Umar M. Shareef, Abdul M. Shareef, Muhammad Show Man, Abu Sarki, Nura Obi, Naziru Ɗanhajiya, Garzali Miko, Diamond Zahra, Momee Gombe, Khadija Mai Numfashi, Bee Safana da German Yola.
Allah ya jiƙan sa, amin.