Sayyada Fati Bararoji za ta yi taron Mauludi tare da naɗin halifancin ta


Sayyada Fati Bararoji za ta yi taron Mauludi tare da naɗin halifancin ta


Jarumar Kannywood Fati Baffa Fagge (Bararoji) ta shirya wani gagarumin taron Mauludi tare da naɗa ta a matsayin Kalifiyar Fadar Bege.


Za a gudanar da taron a ranar Asabar, 21 ga Disamba, 2024 a gidan ta da ke Kuntau Layin Alfindiƙi, Kano.


Za a yi raron na rana ɗaya da dare.


Mata za su fara da rana zuwa ƙarfe 7 na dare, yayin da kuma maza za su fara daga ƙarfe 7 ɗin zuwa abin da ya sauwaƙa.




A wajen taron za a tabbatar wa da Fati da matsayin Kalifiyar Fadar Bege, wanda Sayyadi Munhaminna tare da ɗan’uwan sa Malam Mus’ab za su tabbatar mata.


Shugaban taron dai shi ne Alhaji Sadik Abubakar Ɗangaske tare da tawagar sa.


Sayyada Fati Bararoji tana gayyatar kowa da kowa a wajen wannan gagarumin taron maulidi da za ta gabatar.