Yadda ‘yan damfara suka yi mini kutse cikin asusun banki – Mansurah - NAIJA STICK

Mobile Menu

Powered by Blogger.

Top Ads

More News

logoblog

Yadda ‘yan damfara suka yi mini kutse cikin asusun banki – Mansurah

Dec 11, 2024


Yadda ‘yan damfara suka yi mini kutse cikin asusun banki – Mansurah


Tsohuwar Jaruma Mansurah Isah, ta gamu da iftila’i inda ‘yan damfara suka shiga asusun ajiyar ta na banki suka yi mata ɗauki ɗaiɗai, suka kwashi kuɗi masu ɗimbin yawa.

Mansurah ta shaida wa mujallar Fim yadda abin ya faru, ta ce “An daɗe da samun wannan matsalar sakamakon ba na ganin alat daga asusun ajiyar na tsawon lokaci, kuma na kai ƙorafi ga bankin amma dai haka abubuwan suka ci gaba da tafiya.”


Ta ci gaba da cewa, “Ba zan san yawan kuɗin da aka ɗauka ba saboda an fi wata shida ana ɗauka da kaɗan kaɗan, kuma ni ina shigar da kuɗi ina fitarwa, don haka da fari ban iya ganewa ba, har sai a ‘yan kwanakin nan na nemi bayanai daga bankin sai na ga an yi mini ɓarna sosai, don kuwa kuɗin da aka ɗauka suna da yawan gaske.









“Kuma a yanzu ma da nake magana da kai ina cikin banki ana ta ƙoƙarin yadda za a shawo kan matsalar.

Mansurah, wadda ‘yar kasuwa ce, ta bayyana wannan al’amari da ƙaddara. “Wannan abu ne da ya zama ƙaddara a gare ni, sai dai fatan Allah ya saka mini ya mayar mini da abin da na rasa,” inji ta.

Ta ƙara da cewa, “Amma dai waɗannan mutane sun ja mini asara ba ƙarama ba, sai dai kawai Allah ya saka mini kuma ya kiyaye faruwar haka a nan gaba.”