Yadda Zaku Cike Shirin LEEP: Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta ƙaddamar da Shirin Labour Employment and Empowerment Programme (LEEP) - NAIJA STICK

Mobile Menu

Powered by Blogger.

Top Ads

More News

logoblog

Yadda Zaku Cike Shirin LEEP: Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta ƙaddamar da Shirin Labour Employment and Empowerment Programme (LEEP)

Dec 3, 2024


Yadda Zaku Cike Shirin LEEP: Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta ƙaddamar da Shirin Labour Employment and Empowerment Programme (LEEP)


Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta ƙaddamar da shirin Labour Employment and Empowerment Programme (LEEP) domin inganta rayuwar mutane miliyan 2.2 duk shekara. Shirin, wanda Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu da Ministan Harkokin Ma’aikata, 


Hon. Nkeiruka Onyejeocha, suka ƙaddamar, yana da manufar samar da ayyukan yi miliyan 2.5 a kowace shekara. Ma’aikatar Harkokin Ma’aikata da Ayyukan Yi ce ke jagorantar aiwatar da wannan shiri.  



Shirin LEEP ya ƙunshi matakai huɗu na horaswa kamar haka:  


1. Digital Nomads – Horaswa kan fasahohin zamani da aiki daga nesa.  


2. Vocational and Entrepreneurship Programmes – Horaswa kan sana’o’i da dabarun kasuwanci.  


3. Job Fairs – Samar da haɗin kai tsakanin masu neman aiki da masu samar da ayyukan yi.  


4. Centers for Learning Spaces – Samar da wuraren koyarwa da ci gaba.  


Yadda Zaku Cike  


Domin cike wannan dama, ziyarci shafin yanar gizon da ke ƙasa:  


- Shafin Cikewa: https://leep.gov.ng/join


- Shafin Ƙarin Bayani: https://leep.gov.ng