Za a yi bikin Ai’sha ɗiyar jaruma Asma’u Sani - NAIJA STICK

Mobile Menu

Powered by Blogger.

Top Ads

More News

logoblog

Za a yi bikin Ai’sha ɗiyar jaruma Asma’u Sani

Dec 2, 2024


Za a yi bikin Ai’sha ɗiyar jaruma Asma’u Sani


Cikin ikon Allah a ranar Juma’a, 13 ga Disamba, za a ɗaura auren ‘yar fitacciyar jarumar Kannywood, Asma’u Sani, wato A’isha Ibrahim Yusuf, da angon ta Umar Muhammad Sani.


Za a ɗaura auren ne da misalin ƙarfe 1 na rana a Masallcin Quba da ke unguwar Tunkuntawa a cikin garin Kano.



Asma’u dai ta shirya shagulgula da za a gabatar a bikin wanda ‘yan’uwa da abokan arziki za su taru a yi nishaɗi a yi zumunci.


A cikin tsarin abubuwan da za a gudanar akwai Ranar Ƙauyawa, wato Ƙauyawa Day, a ranar 11 ga Disamba a Gidan Ɗanhausa da ke Titin Sokoto a Nassarawa GRA.


Sai kuma taron yini da za a gudanar a ranar 13 ga Disamba ɗin a Tunkuntawa a wajen da ke kallon Layin Shehu Sani Zaiti kusa da Abubakar Boɗinga Mainama.


Hajiya Asma’u ta ce tana gayyatar kowa da kowa zuwa ɗaurin auren da kuma shagulgulan bikin da za a gudanar daga ranar 11 zuwa 13 ga Disamba.