Cibiyar DemyHealth Clinic & Genomic Medicine zata dauki Ma'aikata - Albashi ₦150,000 zuwa ₦200,000 per Month
Cibiyar DemyHealth Clinic & Genomic Medicine shi ne na farko a Najeriya da ke bayar da ayyukan binciken kwayoyin halitta (Genomic Medicine).
Kamfanin yana da haɗin gwiwa da wani babban dakin gwaje-gwaje na Birtaniya, wanda aka tabbatar da ingancinsa (ISO certified). Suna gudanar da sama da gwaje-gwaje 5000, ciki har da wasu nau’ikan gwaje-gwaje da babu wani dakin gwaje-gwaje a Najeriya da ke yi.
Domin cike wadannan guraben aiki shiyasa Ake neman Ma'aikata a wadannan bangarori guda ukku kamar haka:
1. Medical Laboratory Scientist
2. Administrative Manager
3. Human Resource Personnel
Albashi: ₦150,000 zuwa ₦200,000 a wata.
Yadda za a nemi aiki a cikin wadannan bangarori guda ukku:
Duk mai sha’awar ɗaya daga cikin guraben aikin ya aika da takardar CV zuwa wannan adireshin imel: hr@demyhealth.com, kuma ya tabbatar da cewa ya rubuta matsayin aikin da yake nema a matsayin taken imel ɗin.
Share this article to your friend and family!!