Jarumi a Kannywood, Aliyu Gora II ya aurar da ‘yar sa ta biyu
Tsohon Editan mujallar Fim kuma fitaccen jarumi a Kannywood, Malam Aliyu Abdullahi Gora II, ya aurar da ‘yar sa ta biyu, a ranar Asabar, 28 ga Disamba, 2024.
An ɗaura auren Zainab A. Gora II da abin ƙaunar ta Sadiq Ahmad ne da misalin ƙarfe 1:30 na rana a masallacin Juma’a na Abubakar Mahmud Gumi da ke Malali Low-Cost, Kaduna, bisa sadaki Naira 150,000.
Bayan an ɗaura aure, an yi walima a Gambia Street, inda ‘yan’uwa da abokan arziki su ka halarta. An ci, an sha, an gyatse.
Mahaifin amaryar ya yi wa Allah godiya da waɗanda su ka halarci ɗaurin auren, inda ya ce, “Na gode wa Allah da ya ba ni ikon sauke wannan nauyi. Na gode wa Allah, na gode wa Allah, na gode wa Allah. Kuma gaskiya ina godiya ga ɗimbin mutanen da su ka halarci wannan ɗaurin aure. Waɗanda ban yi tsammani ba ma na gan su. Allah ya bar zumunci.”
“Haka kuma ina godiya ga waɗanda su ka ba ni gudunmawa. Akwai waɗanda su ka ba ni gudunmawa na kuɗi, akwai waɗanda su ka ba ni gudunmawa na addu’a, akwai waɗanda su ka yi mani fatan alkhairi da sauran su, dukkan su masoya na ne. Na gode ƙwarai da gaske. Ubangiji Allah ya saka wa kowa da alkairi,” inji Aliyu Gora.
Allah ya ba su zaman lafiya da zuri’a ɗayyiba.