Shirin AI Academy na Gwamnatin Tarayya na Shekarar 2025
Shin kana son habaka baiwarka tare da fasahar Artificial Intelligence (AI) kuma ka zama jagora a nan gaba?
Gwamnatin Tarayyar Najeriya, tare da hadin gwiwar THE COMMONWEALTH, Intel Corporation, da Ma’aikatar Fasaha, Kimiyya, da Kirkire-Kirkire ta Tarayya, ta bude damar neman shiga Shirin AI Academy na Shekarar 2025.
Amfanin cike wannan Shirin:
- Ana gudanar da shirin kyauta, ba tare da wani caji ba.
- An bude shi ga matasa, dalibai, da ma’aikatan gwamnati.
- Ba a bukatar kwarewa a fannin AI kafin shiga.
Darussan suna kan yanar gizo, kuma za a kammala su cikin watanni 3 zuwa 6 bisa tsarin koyo mai sassauci.
Cancantar Shiga Shirin
Shirin ya bude wa:
- Duk ‘yan Najeriya daga dukkan fannoni na ilimi da aikin yi.
- Matasa, dalibai, da ma’aikatan gwamnati.
How to Apply
Wannan babbar dama ce Ga Masu sha’awar cike wannan su ziyarci shafin yanar gizo na Ma’aikatar Fasaha, Kimiyya, da Kirkire-Kirkire ta Tarayya:
Fatan Nasara da Kuma dacewa domin neman shiga shirin.
Deadline:
30/ January /2025
Share this article to your friend and family !!