Shirin AI Academy na Gwamnatin Tarayya na Shekarar 2025


Shirin AI Academy na Gwamnatin Tarayya na Shekarar 2025  


Shin kana son habaka baiwarka tare da fasahar Artificial Intelligence (AI) kuma ka zama jagora a nan gaba? 


Gwamnatin Tarayyar Najeriya, tare da hadin gwiwar THE COMMONWEALTH, Intel Corporation, da Ma’aikatar Fasaha, Kimiyya, da Kirkire-Kirkire ta Tarayya, ta bude damar neman shiga Shirin AI Academy na Shekarar 2025.  


Amfanin cike wannan Shirin:  


  • Ana gudanar da shirin kyauta, ba tare da wani caji ba.  

  • An bude shi ga matasa, dalibai, da ma’aikatan gwamnati.  

  • Ba a bukatar kwarewa a fannin AI kafin shiga.  


Darussan suna kan yanar gizo, kuma za a kammala su cikin watanni 3 zuwa 6 bisa tsarin koyo mai sassauci.  


Cancantar Shiga Shirin  

Shirin ya bude wa:  


  • Duk ‘yan Najeriya daga dukkan fannoni na ilimi da aikin yi.  

  • Matasa, dalibai, da ma’aikatan gwamnati.  


How to Apply 


Wannan babbar dama ce Ga Masu sha’awar cike wannan su ziyarci shafin yanar gizo na Ma’aikatar Fasaha, Kimiyya, da Kirkire-Kirkire ta Tarayya: 


https://scienceandtech.gov.ng 


Fatan Nasara da Kuma dacewa domin neman shiga shirin. 


Deadline:

30/ January /2025  


Share this article to your friend and family !!